Tauraron dan kwallon AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, ya yi ritaya daga buga kwallo yana da shekara 41

Tauraron dan kwallon AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, ya yi ritaya daga buga kwallo yana da shekara 41

Shahararren dan wasan kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic ya bayyana yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekaru 41, inda ya bar gasar Seria A ta Italiya a matsayin wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a gasar.

Ibrahimovic ya bayyana hakan ne bayan wasan karshe da kungiyarsa ta AC Milan ta doke Hellas Verona da ci 3-1 a ranar Lahadi.

"Lokaci ya yi da za mu yi bankwana da kwallon kafa, amma ba a gare ku ba. A karo na farko da na zo ka ba ni farin ciki, na biyu, ka ba ni soyayya. Kun tarbe ni da hannu biyu-biyu, kun sanya ni ji a gida kuma zan zama Milanista gaba daya rayuwata,” Ibrahimovic ya shaida wa magoya bayan Rossoneri a filin wasa na San Siro.

A baya dai kungiyar ta sanar da cewa za ta gudanar da wani dan takaitaccen biki domin yin bankwana da tauraron dan wasan saboda ba za a sabunta kwantiraginsa a karshen watan nan ba.

Ibrahimovic ya buga wasa a kungiyoyi tara a tsawon shekaru 24 a rayuwarsa, inda ya zura kwallaye 561 a kulob din da kuma kasarsa, a cewar Hukumar Kula da Tarihin Kwallon Kafa ta Duniya.

Ya yi ritaya a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a tarihin kasar Sweden da kwallaye 62 a wasanni 121 na kasa da kasa. Ya yi ritaya daga kwallon kafa na kasa da kasa bayan Yuro 2016 amma ya dawo don kamfen din neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya a Sweden a 2021.

Ibrahimovic ya fadawa wani taron manema labarai jiya Lahadi cewa zai huta kadan kafin ya yanke shawarar abin da zai yi na gaba.

"A halin yanzu, ina so in dauki lokaci kuma in ji daÉ—in abin da na yi. Ba daidai ba ne a yanke shawara cikin gaggawa, akwai motsin rai da yawa a yanzu. Ina so in cire lokacin bazara, in yi tunani sannan mu gani, ”in ji shi.

Post a Comment

0 Comments