Matashiyar Da Ta Watsar Da Aikin Club Kan An Umurce Ta Saka Dantofi (Skirt)

Daga Baba Waziri Net.

Wata ma’abociyar amfani da sahar Twitter mai suna EmpressDaisy ta bayyana yadda ta bar aiki a matsayin mai hidima a wani club din shakatawa da ke Lekki Phase 1 a Legas bayan an nemi ta sanya karamin siket da riga.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewar a darensu na farko an ce su rika sanya kananan Siket da kaya kawai a lokutan aiki.

Lokacin da ta tambayi dalilin, manajan ya ce don faranta wa kwastommi rai idan sun sunkuya a kalli bayansu. 

Ta ci gaba da bayyana cewa albashin aikin ya kasance N20k ne kacal, wanda take ganin abin ya yi tsanani.

Saboda wadannan sharudda, ta yanke shawarar watsar da aikin tun a bayan darenta na farko a bakin aiki.

Post a Comment

0 Comments