Musulunci ya samu gagarumin ci gaba, inda Mace ta farko Musulma daga jihar Kano ta yi Digiri Uku ta zama ƙwararra ‘wajan gano cutuka masu yaɗuwa da magance su’ wato 'Epidemiology' a turance.
Wannan course din dai babban course ne da ake gadara da shi a kasashen duniya.
Ƙasashen da suka ci gaba suna girmama masu wannan karatun domin yadda suke binciken gano cutukan da suke saurin yaɗuwa da kuma samar da mafita ta hanyar da za a magance su.
Dr. Fatima Muhamad Turi, ta kammala digirin ta na uku a Jami'ar lafiya ta ƙasar Iran, Dr. ta ƙware kan sani da gano cutuka masu yaɗuwa da yadda za a magance su (Epidemiology).
0 Comments