Wata Bishiya Mai Dadadden Tarihi Ta Kai Kasa A Katsina.


Daga Mohammad A. Isa.

Wata Bishiyar Kuka mai dadadden Tarihi wadda take a karamar hukumar Batagarawar jihar katsina, ta kai kasa a ranar Larabar nan.

Kamar yadda bayanai suka suka ce, Kukar mai suna 'Kukar Gandu' wadda take da tarihin shekaru sama da 100 a garin, tana a cikin gonar Mallamawan Katsina hakimin Batagarawa.

Kukar ta cimma ajalinta ne inda aka sare ta sakamakon wani Titin (byepass) da za a yi wanda zai biyo ta gefenta, sannan kuma za a yanka wasu filaye a cikin gonar da Kukar take saboda gary ya cimmata.
Kukar Gandun dai na ta tarihi tare da abubuwan ban mamaki a tattare ita. Jaridar Katsina City News ta ta6a fitar da rahoto a kanta dangane da tarihi da kuma abubuwan al'ajabin da ke tattare da Kikar, inda a ciki jaridar ta bayyanar cewar, tsawon shekaru masu yawa babu mutumin da ke iya tunkarar kukar da sunan hawanta in ban da mutum daya tal a garin, shi ma kuma yanzu bai iya hawan naya iya saboda ya tsufa.

Bugu da kari, rahoton jaridar ya bayyanar da cewar idan aka haska Mukar da dare da Tocila, za a ga wasu hasake na bayyana (reflection) daga gare ta, da dai sauran abubuwan al'ajabi da kukar take da su.

Post a Comment

0 Comments