Praymid City FC Ta Duki Dan Ali Nuhu A Makarantarta.

Daga Mohammad A. Isa Da Fagen Wasanni.

Kungiyar nan ta kwallon kafa ta Pyramid City FC ta yi farin ciki tare sanarwar rattaba hannu bisa ga da daukar dan jarumin wasan Hausa na Kannywood, Ahmad Ali Nuhu zuwa Academy din ta.
Hukumar gudanarwar Academy din ta yi matukar farin ciki game da wannan sanya hannun, kuma ta ce tana ganin zuwan Ahmed Ali Nuhu zai karfafa kai harin kungiyar a yayin gudanar da wasanninta.
Har wayau kungiyar ta kara da cewar ta yi imani da yaron zai ci gaba da irin salon wasansa da nasarar da ya samu a yayin zangonsa a garin Fleetwood da ke Burtaniya.

 Hoto: Fagen Wasanni

Post a Comment

0 Comments