NNPC Ya Yi Maraba Da Cire Tallafin Man Fetur.

Daga Zahra Musa 

Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce matakin cire tallafin mai fetur wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi abin farin ciki ne.

Babban Jami’in Kamfanin NNPC Malam Mele Kyari, ya bayyana haka a harabar kamfanin NNPC da ke Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai a daren ranar Litinin bayan sanarwar da Shugaban kasa ya yi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Tinubu, a wajen bikin rantsar da shi a matsayin shugaban tarayyar Najeriya a ranar Litinin din ya ce tsarin cire tallafin yazo karshe  daga zarar gwamnatinsa ta fara aiki.

A yayin da Kyari yake jawabi ga manema labarai ya ce cire tallafin da ya kasance nauyi a kan NNPC zai bada damar samar da kudaden da za’a gudanar da ingantattun ayyuka a kamfanin.

Da yake jawabi game da dogayen layukan da karancin man da ake fama da su, shugaban ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa akawai isassun albarkatun kamfanin musamman man fetur, ya kuma kara da cewa kamfanin yana wadataccen man da zi kai fiye kwanaki 30 a ma’ajiya dan rarrabawa. 

"Babu wani dalilin da zai sa jama’a su firgita, mun fahimci cewa mutane za su ji tsoron sauye-sauyen farashin man fetur, hakan ba dalil bane da zai sa  mutane su yi gaggawar sayen fiye da yadda suke bukata," "in ji shi.

Yayi kira ga ‘yan Nijeriya da kada su firgita  kuma kada su fara siya dan tsoron me zai je ya zo.

Kazalika yace,a matsayin kamfanin na mai samar da mai kamar yadda dokar masana'antar man fetur PIA ta ba da umarni za ta ci gaba da tabbatar da samun PMS da sauran albarkatun mai.

A cewarsa, kamfanin na NNPC yana kuma sa ido a kan dukkan hanyoyin da ake rabawa don tabbatar da bin ka’ida.

Yace “NNPC na tattaunawa da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) don samar da tsarin aiwatar da cire tallafin kamar yadda shugaban kasa ya sanar.

 NAN ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya watan Yuni 2023 a matsayin ranar da za’a cire tallafin man fetur.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa idan ta ci gaba da bayar da tallafin, kasar zata  kashe Naira tiriliyan 6 da biliyan 4 a duk shekara.

Wa’adin da shugaba Buhari ya sanya na cire tallafin man fetur zai zo ne wata guda bayan ya mika wa wanda zai gaje shi a watan Mayun 2023, wanda zai bar sabon shugaban ya magance duk wata cece-ku-ce da hargitsi da ka iya biyo bayan matakin.

Gwamnati ta ce tsarin kashe kudi na matsakaicin zango,shi ne idan aka tsayar da bayar da tallafin man fetur kamar yadda aka tsara a yanzu, za a rika samun kudin tallafina Naira Tiriliyan 6 Bilyan 4 daga watan Janairu zuwa Disamba.

Post a Comment

0 Comments