Daga Wakilinmu Da Dr. Khalid Sunusi Kani.
Matakai ko mu ce abubuwan da ya kamata a fara yi da zarar masu kwacen waya ko makamanta wadannan sun cakawa mutum wuka, su ne kamar haka.
1. Idan sun caka kuma sun zare a ko wanne 6angare ne a jikin bil’adama, to ya zama wajibi ku yi gaggawar samun wani abu mai tsafta ku danne wajen domin sa 'pressure' wacce za ta rage zubar jini.
2. Sannan ku tabbata ba ku tsaya ta kwato waya ba ko abin da aka kwace ba, domin yin hakan zai cutar da wanda aka sokawa makamin. Saboda yawan zubar jinin zai iya hulla shi ya fita daga hayyacinsa, ya fada abin da muke kira da 'Shock'. Zuwa asibiti da wuri (Early Presentation) yana taka rawar gani wajen ceto rayuwar wanda aka lahanta.
3. Ya zama wajibi kar ku dinga jagwalgwala wanda aka sokawa da inda aka soka makamin. Ku tabbata kun kwantar da shi yadda ba zai takura ba; a kwantar da shi ta 6angarensa na hagu (wato Left Lateral Position). Yin hakan na taimakawa zuciya ta tunkud’o jini da sauran ayyuka yadda ya kamata.
4. Idan kuma sun caka sannan sun bar makami a jiki; don girman Allah ka da ku yi yunkurin cirewa! Domin cirewar, zai iya salwantar da rayuwa ta 6allewar jini ya yi ta zuba. Abin da za ku yi shi ne ku nad’e gefe da gefen inda makamin yake wato kusa 'pressure'. Sannan kada ku bari shi ma ya yi yunkurin cirewa da kanshi ko da ba ya jin dadi.
5. Idan son samu ne, ku tanadi wadanda za su iya bada gudunmawar jini tun kuna kan hanyar zuwa asibiti. Yin hakan zai iya rage jan jiki wajen saka jini idan likitoci sun tabbatar da bukatuwar hakan.
6. Don Allah ka da ku cika gaban likita da jama’a. Domin ana bukatar nutsuwa, iska, da yanayi mai kyau duk don ceto rayuwar mara lafiyar da kuka kawo gaban “Likita”.
Mu sni cewa, jama’a da yawa sun rasu domin rashin yin wadannan abubuwa da muka zayyana a sama. Muna mai tabbatar muku cewa idan akai amfani da wad’annan shawarwari, salwantar rayukan zai ragu insha Allah. Har kullum dai “Rigakafi Ya Fi Magani”.
0 Comments