Daga Mohammad A. Isa.
A karo na biyu, Makarantar koyar da karatun Al-kur'ani mai girma ta 'Bin Sa'id Tsangaya Model School' da ke unguwar Tudun 'yanlihidda Katsina, ta yi bikin saukar dalibanta.
Bikin saukar wanda ya gudana a ranar Asabar din nan 7 ga Mayu, 2023, an gudanar da shi ne a cikin farfajiyar wani fili da ke dab da Makarantar, taron da ya samu halartar Iyayen dalibai, Malamai da jami'an gwamnati da sauran manyan baki daga wurare unguwanni daban-daban.
A yayin bikin saukar, an gudanar da Makaloli daban-daban da suka hada da: Makala a kan darajojin Sharifai, Girmama Iyaye, Fifita Karatun Addini A Kan Na Boko, da kuma makala a kan 'Wa dalibi zai yi Abota Da Shi?' da sauransu.
Sauran abubuwan da aka gabatar a taron sun hada da: Karatun Ishriniya, karantawa daliban Allunansu na sauka (Darasu), ba da shaidar Karatun Saukar, ba da shaidar Kammala Islamiyya da kuma hotunan tarihi.
Bugu da kari, Malamai da Iyayen dalibai sun gabatar da jawabai a taron, inda suka ja kunnen dalibai musamman dangane da zage damtse a kan karatu da sauran al'amurran yau da kullum na rayuwar nan ta duniya.
"Ka da ku ga kun yi wannan Sauka ku ga cewa kamar kun gama da Al-kur'ani; a'a yanzu ma ne kuka fara." In ji wani Malami.
"Ku ji tsoron Allah tare da bibiyar Malamai ta hanyar zuwa wasu makarantun (neman ilimi)." Wani Malami ya zaburantar da su.
Daga karshe, shugaban Makarantar Malam Abdurrahim Sa'id ya karanto wasu nasarori da makarantar ta samu tun daga lokacin fara karatu a makarantar zuwa yau, tare da jero wasu kalubale da ke fuskantar Makarantar.
Hakazalika, shugaban ya kuma ya godewa wasu Iyayen dalibai wadanda suke turo 'ya'yansu zuwa Makaranta a kan lokaci tare da biyan kudin Makaranta a kan kari, gami kuma da ba wa makarantar tallafi lokaci-lokaci.
Manyan bakin da suka halarci bikin saukar sun hada da: Alaramma Malam Hafizu Dayyabu Imam, Malam Dangaje (Khalifan Marigayi Malam Sani Mai Gemu gambarawa da Malam Idris Bugaje da sauransu.
Sauran sun hada da: Honorable Ibrahim Idris Safana, Dakta Abdulhakeem Sai'du Gambarawa, Alhaji Nura Garkuwar Malamai, Alhaji Sa'idu A. Habib Gambarawa, Alhaji Abba Sale da sauransu.
A wannan karon dai, Makarantar ta yi wa dalibai 20 cif bikin saukar ne, wadanda suka hada da Maza 8 Mata 12.
1 Comments
Masha Allah. Allah ya yi wa karatu albarka
ReplyDelete