Daga Mohammad A. Isa
Hukumar 'yansandan jihar Katsina a ta bakin mai magana da yawunta, SP Gambo Isa a ranar Alhamis din nan, ya shelanta cewar harkar dabanci wadda Kauraye ke yi da kuma kwacen Wayoyin da zauna-gari-banza ke yi wa al'ummar ta Katsina hukuncinsa daya da ta'addanci a dokance.
SP Gambo Isah ya yi wannan bayanin ne a wani sakon baki (Voice) da ya aiko da shi a zauren 'Nigerian Police Katsina Media' na sahar Whatsapp, a wani jawabi na kara fayyacewa da karin haske kan dokar fashi da Makami a wani yunkuri da hukumar tasu ke yi na kakka6e ayyukan dabanci, Kauraye da kuma kwacen Wayoyi wanda ke ta ta'azzara a jihar.
"Mukaddashin kwamishinan 'yansanda wanda yake rike da wannan runduna ta jihar Katsina, DCP Shettima Mohammed ya karfafi rundunar tsaro da cewar lallai a fita dukkan wata ma6oya da ake ganin wadannan 6arayi da Kauraye suna taruwa musamman a wuraren shaye-shaye da a kai masu farmaki." In ji shi.
Ya ci gaba da cewa "Kuma an karfafi jam'ian da cewa su yi amfani da duk wata dama da suke da ita domin su murkushe wadannan gungun 'yan fashi da suke fitowa da makami suna sarar mutane da kwace masu Waya."
Kakakin rundunar 'yansadar har walau, ya bayyana cewar an ba su damar su murkushe duk wani gungu na wadannan kauraye da masu kwacen wayoyi a cikin lungu da sakon jihar har sai an ga an fidda a'i daga rogo.
"An ba wa jami'an tsaro dama da cewa su yi amfani da bakin bindigarsu" -Ya shelantar.
Hakazalika, SP Gambo Isah ya kuma shelanta cewar an ba su cikakkiyar damar su bi wadannan masu ta'asa har a karkashin gado su kamo su, sannan kuma ya yi gargadi da cewa duk wanda ya ba su ma6oya a gidansa, za a karya kofar gidan a cacukumo shi a gurfanar da shi a gaban Shara'a.
Kakakin ya kara da cewar "wannan shi ne matsayarmu, kuma muna nan muna aiki ba dare ba rana da yardar ubangiji sai mun kawo karshen wadannan 'yan ta'adda." Ya tabbatar.
0 Comments