Kotun da ke sauraren koke-koken za6e a jihar Katsina, ta umurci INEC da ta kwace takardar shaidar lashe za6e daga hannun Salisu Yusuf Majigiri ta mika wa Naziru Bello.
Kotun wadda take sauraren koke-koken za6en da ke cikin babbar kotun tarayya da ke Katsina, ta umurci hukumar za6e mai zaman kanat ta Kasa, INEC, da ta gaggauta kar6e shaidar lashe za6en daga hannun Honorabul Salisu Yusuf Majigiri wanda a baya INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe za6en dan majalisar wakilai ta maza6ar Mashi da Dutsi a jihar Katsina, zuwa ga Honorabul Nazifi Bello, dukkaninsu da suka fito a jam'iyyar ta PDP.
A wata majiyar kuma ta rawaito cewa É“angarensu Majigiri ba su gamsu da hukuncin ba, inda suka bayyana aniyar garzayawa zuwa kotun daga ke sai Allah Ya isa domin tabbatar da nasarar da ya samu tun a farko.
Sauran labari na nan tafe cikin bidiyo game da yadda shari'ar ta kaya.
Hoto: Katsina daily news
0 Comments