Daga Ammar M. Rajab
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya Usman Baba ya bayar da umarnin sauyawa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah wurin aiki kwanaki kadan bayan da ya ci zarafin ‘yar jaridar TTV, Rukayyah Jibia.
A wani mataki da masu bincike ke gani a matsayin hukunci, an mayar da Mista Isah, babban jami'in ‘yan sanda zuwa hedikwatar ‘yan sandan shiyya ta 14 da ke jihar Katsina.
Sabon canja wurin aikin, mai kwanan watan ranar 25 ga Mayu, 2023 kuma mai lamba CH.5360/FS/FHQ/ABJ/V.Til/210, ya shafi jami’an ‘yan sanda 15, inda Mista Isa ke kan gaba.
A kwanan nan ne wata ‘yar jarida a Katsina, Rukayyah Jibia, ta yi tsokaci kan barazanar da ‘yan sanda suka yi mata, bayan ta wallafa wani faifan bidiyo a TikTok, inda ta caccaki rundunar ‘yan sandan jihar Katsina da gurfanar da wadanda ake tuhuma gabanin shari’a.
Ta ce gurfanar da wadanda ake zargin na iya bata sunan su, musamman idan ba a same su da laifi ba kotu ta wanke su ta sallame su.
Ta kuma bukaci ‘yan sanda da su rika bai wa kotu damar hukunta wadanda ake tuhuma ko kuma ta yanke musu hukunci kafin mika su ga manema labarai.
Sai dai shawarwarin da ta bayar ba su yi wa ’yan sandan dadi ba, inda suka zarge ta da yin zagon kasa ga ayyukansu da kin mutunta su.
Karin bayani zai daga baya.
0 Comments