Daga Abul bikra Bbh
Sabrina, wata matashiya mai shekara 22 ƴar ƙasar Malaysiya kuma ƴar rawa salon K-pop, ta ce tana fuskantar ƙalubale sosai daga wajen wasu mutanen da ke ganin bai dace a matsayinta na Musulma tana rawar ba.
Shekara uku da suka gabata ne ta buɗe shafi a safin sada zumunta na sahar YouTube a lokacin da ta koma Koriya ta Kudu daga garinta.
Ba ta daɗe da buɗe shafin ba ta samu mabiya fiye da dubu 200k amma ta ce mu'amalar da wasu masu bibiyarta ke nunawa ba mai daɗi ba ce, musamman a matsayinta na mai saka Hijabi kuma wacce ta yi fice.
0 Comments