Mai martaba sarkin Daura, Alhaji Dr.Umar Faruk ɗaya daga cikin sarakunan Hausawa da su rage, ya bayar da bayyana cewar, daga yanzu Hausawa ba za su yarda wani mai bayar da tarihinsu walau a kafafen watsa labarai ko wani waje ba su ci gaba da alaƙanta batun "Banza" cikin tarihin Hausawa ba.
Sarkin ya sanar da haka ne a lokacin da wata sabuwar kungiyar Hausawan Nijeriya ta kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa da ke Daura a cikin makon nan.
Ya ce abin da ya aminta da shi tare da dukkan sauran Hausawa cikin abin da ya shafi mulkin 'ya'yan Bayajidda shi ne "a kira su 'yan'uwa Bakwai" In ji sarkin.
A yayin da yake tsokaci a kan wannan kungiya ta zpyarce sa, sarkin na Daura ya yi matukar farin ciki da samun wannan kungiyar tare da nuna cikakken goyon bayansa a gare ta, musamman a daya daga cikin manufofin kungiyar na kokarin farfaÉ—o da kima, daraja da samuwar 'yancin Hausawa.
0 Comments