Wata Lauya A Saudiyya Na Son A Kori Ronaldo Daga Kasar.


Lauyar kasar Saudiyya, Nouf bin Ahmed, ta sha alwashin shigar da kara a kan Cristiano Ronaldo bayan da dan wasan ya bayyana damke al’aurarsa a lokacin da yake fita daga filin wasa a ranar Talata.

Lamarin ya faru ne bayan kungiyar Al-Nassr ta Ronaldo ta sha kashi a hannun Al-Hilal na Odion Ighalo da ci 2-0 a daren ranar Talata.

An dauki matakin da Ronaldo ya yi a matsayin cin fuska ga magoya bayan kungiyarsa da ci 2-0

Wani faifan bidiyo da aka fitar a shafukan sada zumunta ya  nuna dan wasan mai shekaru 38 da haihuwa yana sosa Al'aurarsa ​​a lokacin da yake barin filin wasa a matsayin martani ga magoya bayansa da ke rera wakar abokin hamayyarsa Lionel Messi, in ji Daily Mail.

Yayin da take mayar da martani, Nouf ta ce ya kamata a hukunta Ronaldo saboda "laifi na rashin da'a da ya yi a bainar jama'a.

A cewarta, laifin ya hada da kamawa da kora idan wani baƙo ya aikata.

"Ana daukar hakan a matsayin laifin cin mutuncin jama'a, kuma yana daya daga cikin laifukan da suka hada da kamawa da kora idan wani dan kasar waje ya aikata," Nouf ta fada a shafinta na Twitter, yayin da ta sha alwashin shigar da kara ga ofishin mai gabatar da kara na Saudiyya kan laifin da ya aikata na rashin mutuncin jama'a'

Rahoton ya kara da cewa Ronaldo ya kuma sha suka daga ‘yan jarida a kasar Saudiyya, inda Ozman Abu Bakr ya ce Al-Nassr ya kamata ya janye kwantiraginsa na fam miliyan 175 a duk shekara sakamakon rashin da’a da nuna rashin mutunci ga ‘yan kallo.

Sai Dai kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito, majiyar Al-Nassr ta kare Ronaldo da ikirarin cewa ya yi hakan ne bayan da ya samu rauni a lokacin wasan' a al'aurarsa.

Post a Comment

0 Comments