Mai martaba Sarkin Katsina ya naɗa sarauta wa, wasu muhimman mutane a Katsina
Bishir Umar, Suleiman Suleiman Garba @Zamani Media Crew
Mai Martaba Sarkin Katsina Alh. Dakta Abdulmumini Kabir Usman CFR ya naɗa Muhimman Mutane Shida a sarautu daban-daban a gundumar Katsina.
Bikin naɗin da aka gudanar ranar Asabar 29 ga watan Afrilu a fadar Masarautar Katsina dake Kofar Soro ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar Katsina, Irinsu Maigirma Mataimakin Gwamnan jihar Barno, Tsohon Shugaban Hukumar Shige da fice ta Najeriya Alh. baban Dede, da Mataimakin hukumar, Shugaban Rundunar 'Yansanda ta Zone 14 dake jihar Katsina, GOC Alh. Dahiru Mangal, Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Qs. Mannir Yakubu, da sauran manyan baki, masu sarautun gargajiya sarakuna daga wajen Jihar Katsina. Wadanda aka naɗa sun haɗa da,
Sarkin Dawaki Mai Tuta Alh. Sadiq Musa Kaita, Turakin Katsina Alh. Lawal Sani Store, Magaji Riyoji Mannir Husaini, Jagaban Katsina Alh. Tijjani Muhammad Saulawa, Kuliyan Katsina Alh. Muntari Dodo, 'Yandoton Katsina Alh. Mustapha A. Saulawa, sai Riyoji Alh. Jafaru Yusuf.
Sarkin na Katsina ya ja hankali gami da nasiha akan taimako, zumunci da hadakai don aiki tare. Dakta Abdulmumini Kabir Usman yace "Kuso Talaka Kutaimaki Talaka, ku sada Zumunci kuma kusani ni ba nine na naɗa maku wannan nauyi ba Allah ne ya baku ni Dan'aike ne.
0 Comments