Daga Mohammad A. Isa.
Hukumar nan ta Tattara Kudaden Haraji Ta Kasa Reshen Jihar Katsina 'Federal Inland Revenue Service' a turance, ta gina tare da bude katafariyar Asibitin al'umma a Filin Canada da ke Sabuwar unguwa, karkashin Maza6ar Wakilin Kudu ||| a cikin birnin Katsina.
Taron bude asibitin wanda aka gudanar a safiyar ranar Asabar din nan 29 ga Afrilu, 2023 a harabar Asibitin, ya samu halartar gwamnan jihar Katsina mai barin gado, Honorabul Aminu Bello Masari da sauran mukarraban gwamnati.
Da yake jawabi da harshen Turanci a yayin bude Asibitin, shugaban hukumar tattara kudaden harajin na jiha, ya bayyana asibitin wanda hukumar ta gina a matsayi wani tallafi daga hukumar zuwa ga al'ummar jihar katsina, inda suka za6i su gina ta a wannan unguwa duba da bukatuwar hakan ga al'ummar unguwar.
Ya kara da cewa, suna fatan al'ummar unguwar da ma sauran al'ummar jihar katsina baki daya da su ci moriyar Asibiyin, tare da kulawa da ita domin amfanuwar al'ummomi.
Shi ma a nashi jawabin, gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya bayyana gina asibitin a matsayin abar bukatuwa a jihar ta Katsina, inda ya ce; "Muna bukatar irin wadannan wurare na kula da lafiya a fadin jihar Katsina..."
Gwamna Masari ya kuma jinjina wa hukumar bisa ga wannan namijin kokari da ta yi, inda ya jaddada jin dadinsa matuka tare da yi wa al'ummar unguwar fatan cin moriyar Asibitin yadda ya kamata.
Ba garorin da Asibitin ta kunsa sun hada da; Ɗakunan ƙwanciya na Maza, Ɗakunan ƙwanciya na mata, Ɗakin ƙwanciya na Yara, Ɗakin Gwaje-gwaje, Aune Aune da Scanning, Ɗakin Tiyata, Ɗakin kulawa da Haɗurra da Buƙata ta Gaggawa, Ɗakunan kwana na Likitoci, da Ɗakunan kwana na Ma'aikatan jinya.
Sauran sun hadada; Ɗakin ƙwana na Maigadi, Ɗakin cin Abinci, Masallaci, Makewayi na Maza da na Mata, Filin aje motoci, da Kwalta mai tsawon mita 500 da dai sauransu.
Tuni dai an radawa Asibitin suna da "Late Major General Abba Siri-siri 33 Memorial Hospital, Katsina", sunan wanda yake a matsayin girmamawa ga zakakurin marigayi jami'in Sojin nan na jihar Katsina.
A lokacin da Zamani Media Crew ke zantawa da al'ummar unguwar, sun bayyana farin ciki da jin dadinsu ainun, bisa ga samar masu da wannan katafariyar Asibiti.
Su kuwa Iyalan Marigayi Abba Siri-siri wanda Asibitin ke dauke da Sunansa, sun bayyana radawa Asibitin sunan Mahaifinsu a matsayin wata girmamawa ta musamman a gare shi, inda suka bayyana girmamawar wadda ba za su ta6a mantawa da ita ba har abada.
0 Comments