Tare da dukkan girmamawa,
You excellency, ka sani akwai babban kalu-bale a gabanka ga Matasa wajen samar masu da ayyukan yi a za6a66iyar Gwamnatinka.
Alal hakika Matasanmu sun kammala karatun a fannoni daban-daban, ga su nan gungu-gungu amma babu ayyukan yi. Wadanda suka kammala karatun kalilan ne suke da ayyukan yi din, walau na sana'o'in hannu da suka gada ga iyayensu, ko kuma wadanda da suka iya yin fafutika suka samurwa kansu. Su ma kuma suna fama da karancin jarin gudanar da ita yadda ya kamata, matuka.
Your excellency, rashin aikin yi din nan ga matasa ya sa dayawansu suka samarwa kansu ayyukan yi amma na 6atacciyar hanya, wadanda ke kai su fadawa mummunar hanyar ta'addanci da munanan laifuka, kamar harkar Dabanci ko kauranci (da suka addabi jihar), Shaye-shaye wanda ke kashe masu rayuwa da gobensu su rayuwa a matsayin matattu, Sace-sace da dirawa gidajen mutane (wanda ya ta'azzara yansu haka a jihar), da sauran wasu miyagun ayyuka wadanda suke barazana ga tsaron jihar.
Lallai a samarwa matasa musamman wadanda suka kammala karatu ayyukan yi a ma'aikatu da ofisoshin nan da wadanda suke a cikinsu suka yi ritaya, suka zama kamar kufai, sai 'yan kadan daga cikinsu 'yan casual ke zaune a cikinsu, su ma kuma wasunsu ke koken ana rike masu albashinsu watanni kafin a biya su.
A don haka mu a matsayinmu na matasa da muka kammala namu karatun, muke shawartar ka your excellency da cewa ya kamata gwamnatinka ta fi maida hankali a kan matasa kuma maida hankalin na gaske (kamar yadda kake yawan fadin cewa gwamnatinka ta matasa ce), muddin dai kana son ciyar da jihar gaba kamar yadda muke kyautata maka zato kuma muke ganin haka a tafiyarka; domin dai duk harkar da babu matasa, to ba ta da gobe. Haka kuma duk al'ummar da ba ta da matasa, to kuma ba ta da gobe.
Fatan alkhairi a gare ka da gudanar da mulki jihar katsina cikin nasara!
Mohammad A. Isa Katsina, dan jarida mai sharhi kan al'amurran yau da kullum.
0 Comments