BINCIKE NA MUSAMMAN: YADDA JAM’IYYAR PDP TA FAƊI ZAƁE A JIHAR KATSINA
...Labaran da ba a sani ba
...Ribar da Yakubu Lado ya samu.
Daga Wakilanmu 27/4/2023
@Katsina City News da Jaridar Taskar Labarai.
Tun bayan kammala zaɓuɓɓkan 2023 mutane ke ta neman jin me ya faru ga jam’iyyar PDP Har ta kasa taɓuka wani abin kirki a zaɓen gwamna da ‘yan majalisun jiha a Katsina? A zaɓen shugaban ƙasa jam’iyyar ta ɗan tagaza inda ta samu wasu kujerun majalisun tarayya kuma jam’iyyar ce tafi yawan ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasa. Jam’iyyar na a kotu a wasu zaɓuɓɓukan na majalisun tarayya da na sanata.
A zaɓen gwamna jam’iyyar sam bata taɓuka komai ba, ta ƙyale zaɓen ya tafi ne kamar wani bonus da ya sa jam’iyyar APC ta ɗauki jihar a sanga. Zaɓe ne aka yi ganganariya ba tare da wata turjiya daga jam’iyyar adawa ta PDP ba akwai ‘yan majalisun dokoki ɗaya zuwa biyar, ‘yan takarkarin daga jam’iyyun PDP da NNPP da PRP sun yi ƙoƙararin kawo kujerun su amma suka kasa.
Me ya faru a zaɓen na farko na gwamna da ‘yan majalisun jiha?
Mun yi zurfin bincike akan abun da ya faru, mun yi magana da mutane da yawa a cikin PDP don wannan rubutu, wasunsu manya ne a cikin tsarin kamfen na Sanata Yakubu Lado wasu kuma ‘yan takara ne da suka faɗi zaɓe, wasu matasa ne wasu dattawa ne a jam’iyyar. Wannan labarin mun ɗan tsakuro shi ne daga waccan tattaunawar da muka ɗau tsawon kwanaki mu na yi da mutane daban -daban.
Bayan kammala zaɓen gwamna jiga-jigan jam’iyyar PDP sun kira wani taron manema labarai a ofishin kamfen ɗin su dake daura da filin wasan Karakanda a wajen taron na manema labarai jam’iyyar ta tabbatar wa duniya cewa, su da ɗan takararsu za su tafi kotu su ƙalubalanci zaɓen. Ɗantakarar gwamna na jam’iyyar ya amshi abun magana ya tabbatar da cewa lallai zai je kotu.
Tun kafin a shigo taron na manema labarai jiga-jigan jam’iyyar da kuma kwamitin kamfen ɗin suka tambaye shi a wajen mitin ka shirya zuwa kotu? Ko ko jam’iyya ce zata tafi? Sanata Yakubu Lado ya tabbatar masu da cewa a shelanta cewar shi da jam’iyya za su tafi kotu. Bisa amicewarsa aka yi waccan shelar ta zuwa kotu, kamar yadda wani da aka yi zaman da shi ya tabbatar ma wakilanmu.
“Haka muka saki jiki ɗan takara zai ɗau lauyoyi waɗanda za su shirya hujjojin tafiya kotu sai da ana sauran awa 48 a rufe duk wani ƙorafin zuwa kotu, sannan ɗan takara yace ya sauya zuwa kotu ba za a je kotu ba, dukkaninmu muka shiga halin kiɗima, babu lauyan da zai iya shirya ma jam’iyya ƙorafin kotu cikin awa 72 yanzu saura awa 48 kamar yadda dokar zaɓe ta bayar cikin bakin ciki muka kwana ana wayoyi”. In ji wani jami’in kamfen kwamitin yaƙi neman zaɓe na PDP da mu ka yi magana da shi.
Me ya hana zuwa kotu? Da kuma boye wa jam’iyyar PDP har lokaci ya ƙure?
Zarge-zarge na ta yawo waɗanda jaridun mu suka tabbata daga mabambanta bakuna, wani ɗan kwamitin kamfen ya bamu bayanin shi da cewa,
“Tun muna kamfen labarai kan zo mana cewa ɗan takarar PDP shi ne babban ɗan kwangilar gwamnatin tarayya daga jihar Katsina, musamman a ma’aikatar ayyuka ta gwamnatin Tarayya, ana kamfen mun riƙa jin labaran yadda kwangiloli ke shigo masa, nan a tsakaninmu muka fara tunanin an ya kuwa ba mun fada “One chance ba”? ya za a yi hukumar gwamnatin tarayya ta riƙa ba ɗan adawa wanda ke ƙalubalanatar jam’iyya mai ci kwangila? Sai dai in akwai wata a ƙasa?”.
Zargin da mafi yawan yan PDP ke yi akan ƙin zuwa kotun Lado shi ne an yi wata yarjejeniya ce tsakanin shi da wasu a gwamnatin tarayya, wasu kuma na ganin a a ya rama ma kura aniyarta ne yana amsar kwangilolinsu an faɗi zaɓe ya ƙi zuwa kotu ya kuma shamci jam’iyya yadda babu yadda za ayi taje kotu.
Dukkanin manyan jam’iyyar PDP da mu ka yi magana da su sun tabbatar mana babu in da Yakubu ya kira taro don tattauna ƙin zuwa kotu da kowa sakon waya ne na minti daya ya faɗi wa wani jigon jam’iyyar cewa babu zuwa kotu ka faɗa wa saura daga nan bai ƙara ɗaukar wayar kowa ba. Kamar yadda aka tabbatar mana.
KO YAKUBU LADO DA GASKE YA SHIGO TAKARA?
Wani jigo a kwamitin kamfen, ya faɗa mana cewaa, bayan fitowa takararshi da abin da ya biyo baya PDP ta rabu uku, waɗanda suka fice daga jam’iyyar irin su Hamisu Gambo Ɗanlawan Katsina, sai ɓangaren Shema da suka ƙi shelanta fita daga jam’iyyar amma suka riƙa yi mata zagon ƙasa, sai waɗanda suka tsaya a jam’iyyar su ka yi aiki da zuciya ɗaya tsakaninsu da Allah. “Danjuma haka muka zauna mu kai ta amsar wuta ba wanda ya sani sai dai mu goge zufa muyi shiru” inji mai bamu bayanin.
“Waɗancan ‘yan uwannamu guda biyu sun riƙa gargaɗinmu da jawo hankalinmu mu riƙa taka tsantsan da kuma sara muna duban bakin gatari amma duk bamu ji ba, abin kamar ɗaurin baki’’
Duk jami’an kwamitin yaƙin neman zaɓensa sun tabbatar mana har aka gama yaƙin neamn zaɓen zuwa zaɓe, Yakubu Lado bai kama wani ofis ɗaya ba na kamfen ɗin shi duk wani ofis da ka gani ba shi aka yi bai taɓa sayen wata mota don kamfen ba, bai taba sayen koda babur na hawa ba ya rabar don kamfen na shi, “baya da wani ofishi daga jiha zuwa ƙananan hukumomi na zaɓen shi ka taɓa ganin an nemi zaɓen gwamna a haka?” Inji wanda ke bamu bayanin shi.
Wannan zargin na ƙin kama wani ofis ko sayen abin hawa mun yi iyakar bincikenmu mun gano haka ne. abin da bamu samu tabbaci ba ko yana mayar da kuɗin haya ga waɗanda sukan bashi ofis ko kuɗin motocin da aka ba shi.
Kuma a binciken mu mun ci karo da waɗanda suke iƙirarin sun yi amfani da kuɗaɗensu domin kamfen ɗin an ce za a biya su amma har yanzu shiru kuma basu san wa za su riƙe ba? Wasu suna ta saƙar zuci akan ya za su yi?
Wani zargin kuma shi ne takura kuɗin hidimar kamfen, Har aka gama kamfen na yankin Funtua duk wani kuɗin hidimar yankin Yakubu bai kowa ko sisi ba, sau da yawa mutane suka riƙa amfani da kuɗaɗen bisa tsammanin za a biya su.
Kuɗin kamfen ɗin baki ɗaya shi ne yake bayar da su da kanshi don haka, ya tsara kuma yana bayarwa ne yadda ya so, wani lokaci kuma yana amfani da ‘ya’yanshi wajen bayar da kuɗin ko kayan zaɓen kamar yadda muka samu tabbaci
Ana gobe zaɓe akwai muhimman kuɗaɗen aikin zaɓen ya riƙe yaƙi sakin su wanda wannan ya taimaka wajen faɗuwa zaben, ‘yan takarkarin wasu mukamai aka ƙi taimakon su suka zama marayu a ranar da suke buƙatar mataimaki.
KO NAWA YAKUBU LADO YA KASHE?
Mun ga kasafin kuɗin da aka tsara za a kashe a zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna wanda sam ba ayi amfani da shi ba, wani ɗan kwamitin yaƙin neman zaɓen a ofis din kamfen na Atiku Abubakar ya tabbatar mana.
Bayan ƙiyasin duka biyu muna iya tabbatarwa cewa Sanata Yakubu Lado yaci ƙazamar riba a wannan zaɓen na 2023. Akwai kuɗaɗen da ba wanda yasan nawa aka ba shi, ta tabbata Atiku Abubakar ya ba shi gudummmuwar zaɓen shi, haka ma wasu gwamnoni PDP wanda shi kaɗai ya san nawa ya samu. Sai kuma ɗai-ɗai ku da su ka yi ta kawo ɗaukin gudumuwa yana amsa. Da kuɗin zaɓen shugaban ƙasa, dana gudummuwar takarar gwamana Yakubu bai kashe kashi arba in cikin ɗari na abin da ya tara ba. Sannan ga ribar ƙin zuwa kotu wanda wannan shi kaɗai yasan me za ya girba.
“kamar ɗaurin baki sai da muka kai iya ruwa tsakiya muka ankara cewa, yaron nan yana mana wasa da hankali kuma shi kasuwanci ya kawo shi amma daidai lokacin bakin alƙalami ya riga bushe, sam takarar ba da gaske bace, muna taro da shi da rana in dare ya yi. Ya yi taro da wasu”. Inji wata majiya mai tushe.
Rigimar kuɗin zaɓe yanzu haka tana gaban kotu, kuma an tabbatar mana kwamitin dattawan jam’iyyan suna neman dole sai yazo ya yi bayanin su.
BAHASIN LADO AKAN ZARGE -ZARGEN
Mun yi iyakar ƙoƙarin mu domin jin ta bakin Sanata Yakubu Lado Danmarke mun kasa, mun kira wayarshi sau talatin bai ɗauka ba. mun aika masa da saƙon waya. Ya bamu amsa kamar haka “bani nan sai na dawo’’ mun aika masa sako na biyu cewa a waya muka son tatttaunawa ba dole sai mun haɗu fuska da fuska ba, bai bamu amsa ba, mun sake kiran shi bai ɗauka ba.
Duk lokacin da muka same shi zaku ji amsar shi.
Danjuma Katsina ya jagoranci wannan binciken kashi na farko.
Katsina City News
0 Comments