An Ga Watan Shawwal A Hukumance A Nijeriya



Daga Auwal Isah.

Rahotanni daga fadar Sarkin Musuli?in Nijeriya da ke Sakkwato na nuni da cewa, gobe juma'a 21 ga Afrilun 2023 zai kasance 1 ga Shawwal.

Majalisar ƙoli mai kula da harkokin addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin mai Alfarma sarkin musulmi Sultan Abubakar Sa'ad CFR mni ta bada Sanarwar tabbacin ganin watan Shawwal a wasu sannan jihohin Nijeriyar.

"A gobe Jumu'a 21, ga watan Afrilu 2023, shi ne ranar Sallah wanda shi ne zai kama 1, ga watan Shawwal na shekarar 1444H" in ji sanarwar

Allah ya kar6i Ibadunmu ya sa mun yantu daga zunubbai da wutar mahalicci a cikin wata mai fita, ya kuma nuna mana na wasu shekaru masu zuwa.

Da fatan za a yi shagulgulan Sallah Lafiya.

Post a Comment

0 Comments