Katsinawa Ku Fito Ku Zaɓi Atiku Da Surajo Makera Da Chindo A Ranar Asabar Domin Gina Sabuwar Najeriya, Cewar Musa Gafai, Shugaban Kungiyar Ladon Alkhairi
Shugaban shahararriyar kungiyar nan mai rajin tallata yan takarar da jam'iyyar PDP ta tsaida a kowane matakai, karƙashin jagorancin hazikin matashin nan, Honarabul Musa Yusuf Gafai ta yi kira ga al'ummar jihar Katsina, musamman na ƙaramar hukumar Katsina da su fito ranar Asabar mai zuwa domin yi wa yan takarar da jam'iyyar PDP ta tsaida ruwan kuru'u, domin gina sabuwar Najeriya da wakilci na gari.
Honarabul Musa Yusuf Gafai, wanda kuma shi ne Daraktan Matasan yaƙin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar da dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattauna wa da manema labarai a Katsina, yau Laraba.
Hazikin Matashin mai son ganin rayuwar matasan jihar Katsina ta inganta, ya kara da cewa ina neman alfarmar masu zabe da su zaɓi nagartattun yan takarar da jam'iyyar PDP a ranar Asabar mai zuwa, inda za su zabi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa da Alhaji Surajo Aminu Makera a matsayin Sanatan Shiyyar Katsina ta tsakiya da kuma Honarabul Aminu Chindo a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina ta tsakiya, waɗanda da yardar Allah ba za su ba mu kunya kuma ina da yakinin za su gudanar da kyakkyawan wakilci.
0 Comments