A yau 17- 2- 2023 Sanatan Shiyyar Daura kuma mai neman tazarce a kujerarshi ta Sanata karkashin inuwar Jam'iyyar PDP ya gudanar da kamfen dinshi a karamar hukumar mashi a fadin ward dinta gaba daya.
Sanatan yace " Jamiyyar APC babu wata tsiya a cikin ta sai yaudara kuma shine babban dalilin yasa na guje ta, tun ina wata bakwai a ciki aka fara fada dani saboda wlh ba gaskiya sukeso ba kuma ba al'umma ke gabansu ba.
A gundummar Majigiri Sanata Babba kaita yace" Majigiri garina ne saboda Alh Salisu majigiri aminina ne. Anan ba kamfen muka zo ba munzo mugaisa da ku ne saboda alada da akasaba amma garin majigiri garin PDP ne ko da akayi maja a 2015 APC bataci majigiri ba
Shugaban Jam'iyyar PDP na gundummar Majigiri ya fadima Sanata Babba kaita ayyukan da gundummar su sukeso santan ya diba yuwuwar kawo masu dan cigaba da morar damakaradiya kamar yadda sanatan yasaba kawo masu
A duk sauran gundumomin ma Shuwagabanin PDP na gundumomin sun. Nemi Alfarma a wajen dan takarar na ayyuka daban daban wanda ya tabbatar masu da insha Allah zaa diba su.
Sanatan yace " wannan itace karamar hukuma ta bakwai da muke kamfen dina amma wallahi ba inda aka cemana ba'ayi saidai san barka da fatan Alheri akemana na tabbatar da al'umma PDP suke a Jihar katsina dan Babu abinda Jam'iyyar APC tayima al'umma jihar katsina sai yaudara. Yaushe rabon da abaku talk,biyan kudin jarabawa dama sauran abubuwan more rayuwa, Dama wannan PDP tasaba yin su, kuma ni iya yar APC danayi Allah yayafemani saboda an yaudari Al'umma.
Sanatan yakara da cewa " Akwai wasu asibitoci da aka gina a shiyyar Daura amma jam'iyyar APC taki bari a bude su saboda banbancin siyasa da muke da ita dasu amma idan mun anshi mulki ina mai tabbatar maku Insha Allah zaa budesu a cigaba da diba marasa lafiya
Sanatan ya samu rakiyar Alh Salisu Yusuf Majigiri tare da dan takarar majalisa jaha a karamar hukumar Mashi Tare da wasu sauran jiga-Jigan yan Jam'iyyar PDP na karamar hukumar mashi.
0 Comments