Yadda Ta Kaya A Taron Ganawa Da 'Yan Takarkarin Gwamnan Jihar Katsina.

Daga Mohammad A. Isa

A taron zauren jama’a da aka gudanar, na ganawa da ‘yan takarar gwamnan jihar Katsina a ranar Asabar 14 ga Janairu, 2023, don jin k'udurori da aniyar da 'yan takarar suke da ita ga al’ummar jihar katsina da za su aiwatar da zarar Allah ya ba wa mai rabo sa’a a cikinsu na darewa kan kujerar gwamnan jihar ta Katsina, daukacin ‘yan takarkarin sun yi filla-filla da kudurinsu a gaban bainar jama'ar jihar Katsina.
Taron ganawar wanda rukukun gidajen yada labarai na Media Trust da CDD hadin gwiwa da Katsina City News, Vision Fm da Gidan Talabijin na Farin wata suka shirya, ya samu halartar dubban mutanen jihar Katsina wadanda suka hada da kungiyoyin dalibai da sauran al’umma, ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, masu fada-a-ji, ‘yan kasuwa, jami’an tsaro da kuma ‘yan jaridu.

Taron dai an soma gabatar da shi ne da misalin karfe 10:00 na safe a dakin taro na hukumar kula da kananan hukumomin jihar katsina da ke kan hanyar zuwa karamar hukumar Kaita.

Farfesa Sani Abubakar Lugga shi ne uban taro, kuma shi ne ya soma da gabatar da jawabi a taron, in da ya hori ‘yan takarar da cewa su ji tsoron Allah a yayin gudanar da mulkin al’umma, sannan su kuma yi aikin da zai kawo ci gaba mai dorewa ga al’ummar jihar ta katsina.
Shu’aibu Mungadi dan jarida mai sharhi kan al’amurran yau da kullum daga gidan talabijin na farin wata, shi ma a nashi jawabinsa ya ja hankalin ‘yan takarkarin da cewa su tabbatar sun bayyana tare da zayyano kudurori wadanda za su iya aiwatarwa idan sun cimma gaci, domin muddin wani dan takara ya ‘ki aiwatar da kudurin da ya fadi ga mutanen wannan zaure, to fa mu ‘yan jaridu mun taskace su, kuma za mu ci gaba da zakulo su mu yi ta fadawa al’umma, domin kuwa baki shi ke yanka wuya.
Samar da Tsaro, habaka harkokin kasuwanci, inganta noma, samarwa matasa aikin yi, tsari na musamman ga Iyaye Mata, ababen more rayuwa, inganta hanyoyin sufuri, inganta harkar koyo da koyarwa, kawo kwararru a fannin kimiyya da fasaha su ne muhimman kudurorin da ‘yan takarkarin sukai ta kai-komo wajen bayyanarwa a zauren taron.
Abin da muka lura da shi a wajen shi ne, ‘yan takarar sun yi iya kokarinsu wajen kare muradan da suka zayyano musamman a yayin amsa tambayoyi mahalarta. Sai dai a yayin tattaunawarmu don jin ra’ayin mahalarta kan wanda suka fi gamsuwa da kudurorinsa, sun fi bayyana mana wasu kadan daga cikin ‘yan takara da cewa su ne suka fi kawo kudurori bisa tsari da kyau, kuma suka kare su bisa gamsasshiyar hujja da dalili a yayin amsa tambayoyi a zauren.
‘Yan takarkarin Gwamnonin daga jam’iyyu 7 ne suka halarci tattaunawar, wadanda suka hada da; Dr. Dikko Umar Radda daga jam’iyyar APC wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Honorabul Faruk Lawal Jobe, Sanata Yakubu Lado Danmarke daga Jam’iyyar PDP, Injiniya Nura Khalilil daga jam’iyyar NNPP wanda ya samu wakilcin Dr. Muttaka Rabe Darma, Imrana Jino daga jam'iyyar PRP, jam'iyyar BUT wadda Malam Kabir Kofar Bai ke wa takara, Ibrahim Zakari Talba daga jam'iyyar SDP wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, da kuma Dantakarar gwamna daga Jam'iyyar Zenith Labour.

Post a Comment

0 Comments