Za Mu Shiga Lungu Da Sako Sai Mun An Rantsar Da 'Yan Takarkarin Jam'iyyar APC, In Ji Hamisu Gambo.

Daga Mohammad A. Isa, Katsina.

Tsohon dan Majalissa wanda ya wakilci Katsina ta tsakiya a Majalissar Wakilai ta Kasa, Dan Lawan Katsina Honorabul Hamisu Gambo, ya bayyana cewar za su kai gwabro su kai mari har sai sun ga an rantsar da 'yan takarkarin jam'iyyar APC a za6ukan shekarar 2023.

Dan Lawan Katsina ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a yayin kar6ar ziyarar da kungiyar 'Dan Guruf Support For Tinibu2023' suka kai masa a Lambunsa a ranar Lahadin nan.

Honorabul Hamisu Gambo ya ce, akwai shirye-shiryen da suke yi na ganin jam'iyyar ta APC ta cimma gaci, shirye-shiryen da ya bayyana cewar a yanzu ba zai fade su tukunna, domin bai kai ga kar6ar Tikitin jam'iar ba wadda bai jima da yi mata mubayi'a ba, amma a cewarsa za a ga aiki da zarar ya kar6i Tikitin.

Dangane da 'yan takarkarin jam'iyyar na APC kuwa, Dan lawal ya bayyana cewar sai sun tabbatar da sun kawo Kujerunsu a shekarar 2023.

"Za mu shiga Lungu da Sako sai mun ga an rantsar da wadannan mutanen da Aminu Hello Masari ya kawo." - In ji shi

Post a Comment

0 Comments