Tsohuwa 'Yar 150 Ta Bayyana Yadda Sana'ar Tuwo-tuwo Ta Yi Mata Gata A Rayuwa.


Daga Mohammad A. Isa Da Ibrahim Tukur Garkuwa

Wata Dattijuwa 'yar shekaru 150 a duniya mai suna Hajiya Asibi 'Yardukusuru 'yar asalin karamar hukumar Jibiya da ke jihar katsina, wadda yanzu take zaune a 'yar kasuwa cikin birnin katsina, ta bayyana yadda sana'arta ta tuwo-tuwo wadda shafe shekaru aru-aru tana yi ta huce mata takaici a rayuwa har ma da doriya.

Hajiya 'Yardikusuru ta bayyana haka ne a yayin da take amsa tamboyin wakilan tashar watsa labarai ta 'Zamani Media Crew' a cikin wani shiri mai suna "Hatsin Bara" na wannan Makon.

"Ban taba haihuwa ba, amma da sana'ar Tuwo na yi wa 'ya'yan dangi guda tara aure.

"Nan cikin garin katsina, na yi gida ya kai guda biyar. Nan 'yar kasuwa, na yi shago guda 4, amma yanzu ba ni da su duk na sayar. Kuma yanzu ina da gida, ga shi nan(kun gani) wanda nake ciki." In ji ta.

Ta ci gaba da cewa, "Na mallaki motoci Shida; Urban guda biyu, kwamfuta guda hudu. Duk motar da ka gani a da an rubuta miyatti Allah, tawa ce." Ta tabbatar

'Yardukusuru ta ci gaba da cewar, ta je aikin hajji sau shida. A yayin da take bayyana da abin da ta fara kasuwancin nata da shi a matsayin jari tun a lokacin, ta ce duka-duka da naira dari biyu ne ta fara a matsayin jarin a lokacin Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello.

"Na je Makka sau shida. Na far da jari na jikka biyu (naira dari biyu) kudinmu na da. Ko zuwana Makka na farko, abin da na biya jikka hudu da rabi, kudin guzuri jikka biyu da rabi. Haka na biya."

Ta kara da cewar, daga baya ta kara da wasu sana'o'in masu alaka da sana'ar tuwo-tuwo din wanda take yi, kamar sana'ar sai da Shinkafa da Doya, da Naman Kaji da na Zabbi.

Hajiya Asibi 'Yar dukusuru haifaffiyar garin sabon gari ce da ke a karamar hukumar jibiya, inda yanzu haka take zaune a unguwar 'yar Kasuwa da ke cikin birnin Katsina.

Post a Comment

0 Comments