A satin nan ne aka gayaceni taro wanda aka ce taron jam'iyyar PDP ne kuma naje taron ne dan kaunar da nakema jam'iyyar mu ta PDP bayan zuwa na naji ana cewa wai zamu bar tafiyar jam'iyyar PDP mukoma tafiyar Jam'iyyar APC wanda abinda suke fadi bama mai yuwa bane.
Yanzu nakara yadda da maganar Jagora Dr Mustapha Inuwa na cewa Jam'iyyar APC suna iya zuwa da yaudara kala-kala tabin wata siga a hada taro a dauki hotunan Ku ace kun koma jam'iyyar APC.
To ni Jazuli Malumfashi inaso in tabbatarma Duniya ina nan Jam'iyyar PDP ba gudu ba ja da baya kuma Insha Allah sai mun daura dukanin yan takarar mu a kan mulki.
Daga karshe ina kira ga mutanen mu na jam'iyyar PDP da su kula da yaudarar da jam'iyyar APC ke yi su guji kiran taron da basu sansu ba dan ance taron PDP ne kamar yadda na fada tarkon su.
Nagode mhd Jazuli hamza Malumfashi
Shugaban Kungiyar Danmarke Restoration FKD
0 Comments