AN DAGE TARON GANAWA DA 'YAN TAKARKARIN GWAMNA NA KATSINA
Mu'azu Hassan
An dage taron 'yan takarkarin Gwamna na Jihar Katsina, wanda jaridun KATSINA CITY NEWS da rukunin gidajen rediyon VISION FM da gidan talabijin na FARIN WATA suka shirya.
Dagewar ta taso ne sakamakon zama da kwamitin shirya taron ya yi ne a ranar Litinin da ta gabata, wanda taron ya tattauna kara inganta taron da tabbacin halartar wasu manyan dattawan Katsina, tare da kara ba kungiyoyin masu zaman kansu damar su kara shirya wa halarta taron.
Kazalika dagewar za ta bai wa 'yan takarkarin damar shirya wa halartar taron.
A kan haka, kwamitin ya amince da dage taron zuwa wani lokaci cikin watan Disamba.
Dukkanin bangarorin da ke shirya taron sun amince da tsarin, wato KATSINA CITY NEWS da rukunin gidajen rediyon VISION FM da FARIN WATA TV.
Haka kuma shugabannin taron, Farfesa Sani Abubakar Lugga da kuma Malam Abubakar Kabir Matazu duk sun amince da dage taron.
Kwamitin ya tattauna da 'yan takarkarin kai tsaye a wajen taron, inda su ma suka amince da tsarin dage taron.
Kwamitin shirya taron ya tsara ganawa da 'yan takarkarin kafin ranar taron domin bayyana masu tsarin taron da yadda zai gudana.
Masu shirya taron sun tabbatar da cewa dagewar za ta ba mutane da yawa a ciki da wajen Katsina damar halartar taron domin ji da gane wa idanunsu.
0 Comments