Dr Mustapha yace" yan waccen tafiyar Suna cima mutanen mu zarafi ta hanyar yi masu posting a wajen aiki kokuma tunkarar su da kudi dan su bar tafiyata akwai wadda suka kaima miliyan Biyar a ofis wai tabar tafiyata ta dawo tasu da yake idan Allah yasan zuciyan bawansa haka ta dako kudin takawo Mani tace kaga abinda suka bani na bar tafiyar ka, nace tadauki kudin nan ta maida masu. To bama wannan ba akwai wanda suke tuntuba dayawa mutanen mu dandai subar tafiyarmu sai suce aa Ku fara magana da wane.... Sai kaji sunce masu kaji yan tatsine to mutanen mu ba yan tatsine bane ammana Che tsakanin mu kuma insha Allah Zamu rike ma juna ammana.
Dr yacigaba da cewa akwai abubuwan da yan wacen tafiyar sukeyi yanzu sai suce Zawiyya ko Alheri Danko na kiran meeting da kunje sai kuga basu bane su dadauke ku hoto sai bayan kuntafi sai su watsa hoton nan su ce wadanan sun bar tafiyar Dr Mustapha sun dawo wacen tafiyar, to inasu mutanen mu su lura kudai kunsan suwaye Zawiyya ko Alheri danko koma wata kungiya tamu to kutabatar da sune suka kiraku sannan ku halarci taron.
Abinda muka sani faduwa zabe bashi bane karshen siyasa nayi takarar gwamna Allah baibani nasara ba kuma dama munemi Alheri to mun yadda haka shine mafi Alkhairi agaremu, amma bamusan waye mafi Alkairi ba a jihar katsina.
A sati mai zuwa idan Allah ya kaimu zamu fadima Al'umma matsayar mu a siyasar jihar katsina saboda ko yanzu akwai kwamiti da ke tataunawa da inda zamu marawa baya saboda yanzu haka sunyi zama na daya, mun sa ran zasuyi zama na biyu a wannan satin wanda muke sa ran shine na karshe zamu pito mu bayana ma Al'umma matsayarmu walau sabon jariri za'a haifa ko a kasin haka mudai kullum burin mu ina AI'umma suka karkata to nan muke saboda mu Al'ummar ne a gabanmu
0 Comments