Siyasa Rigar Yanci: Yanzu an wuce lokacin siyasa da addini domin cusa mana mutanen banza lalatattu a mulki.



Daga Muhammed Ismail Ali

Naji wani Dan siyasa a wata jaha yace, "Faduwar siyasa ta su Bola da kasim tamkar faduwar musulunci ne" da farko wannan ba abun mamaki bane a gun yan siyasa, domin ko a coci ya shiga haka zai fada, saboda cimma burin sa na daura kowani dan siyasa duk lalacewar sa, muddin zai cusa dollars.

Abunda nake son talakawa su gane shine, wadannan yan siyasa da ake zuzutasu da sunan musulunci, a tsawon rayuwar su wani aiki ne sukayiwa musulunci da har ake ga faduwar su a zabe faduwar musulunci ne?

Dan haka talaka dan uwana ka shiga taitayin ka, kada da zabi rubabbu wallahi idan muka sake muka zabi wadannan sai mun gwamnace Buhari sau million, domin duka rubabbu ne, babu naci a cikin su.

Dan haka ka zabi Atiku Abubakar a zabe mai zuwa babu wani dan takara Wanda a halin yanzu damu yan arewa zamu zaba Wanda ya wuce Atiku saboda shine Wanda ya shiryawa shugabancin Nigeria.

Har ga Allah bani da mutumin da zan zaba a 2023 daya wuce Atiku.

Wallahi Bola mulki baiyi kama dashi ba, kuma yanayin sa yaje ya huta ba mulki ba, jiki duk rawa yake, yaka mata a tausaya masa koda shi bai tausayawa kansa ba, kada a zabe shi.

Allah ya zaba mana shugabanni mafiya alheri.

Post a Comment

0 Comments