Limamin da ya É“oye kiristoci da malamin da ya jajirce kan É—alibansa a hannun Æ´an ta'adda sun shiga jerin wadanda Buhari zai karrama.
Sheikh Abdullahi Abubakar, malamin addinin Islama a jihar Plateau, yana É—aya daga cikin mutane 437 da gwamnatin tarayya ta tantance domin basu lambar girma ta kasa. An zabi Abubakar don karbar lambar yabo ta MON.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai bayar da lambobin girman a ranar 11 ga watan Oktoba, a fadar gwamnati dake Abuja.
An ce Abubakar ya ɓoye Kiristoci 262 a cikin masallacinsa lokacin wani rikici da ya ɓarke a a wasu kauyuka 10 a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau a watan Yunin 2018.
Da ya ke magana kan lamarin, malamin ya bayyana hakan a matsayin "wasan sadaukar da rayuwarsa".
“Ban taÉ“a fuskantar mummunan tashin hankali irin wannan ba a rayuwata. Mummunan lamarin na baya-bayan nan ba a taba ganin irinsa ba,” inji shi.
Matakin nasa ya samu yabo sosai a fadin duniya, kuma a shekarar 2019, an sanar da malamin a matsayin daya daga cikin wadanda suka samu kyautar 'yancin addini ta duniya.
Haka kuma a cikin jerin sunayen da aka saka akwai Muktar Gulma, malami da aka ce ya dage da tsayawa kan dalibansa a wani hari da aka kai a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi, inda bayan Æ´an ta'addan sun sake shi, sai ya ce sai ba zai tafi ba sai da É—alibansa.
An ce a karshe an sake shi tare da wasu daliban.
Gulma yana cikin jerin sunayen wadanda aka zaba domin samun lambar yabo na MON.
0 Comments