Sadio Mane Yana Zuwa Taya Mu Wanke BanÉ—akin Masallaci - Limamin Liverpool

Abubuwan alkhairin da ɗan wasan ke yi na da matuƙar yawa, kuma ya sha samun shaida mai kyau akan riƙon sa da addini.

Shahararren ɗan wasan nan na ƙasar Senegal Sadio Mane ya sha yabo sosai bayan an bayyana wani muhimmin aikin alkhairi da yake yi.

Sadio Mane wanda yanzu haka yana taka leda a ƙungiyar Bayern Munich ta ƙasar Germany bayan ya baro ƙungiyar Liverpool ta ƙasar Ingila, ya samu wannan yabon ne daga limamin wani masallaci a birnin Liverpool.

Limamin masallacin ya bayyana cewa duk da É—aukaka da tarin dukiya da É—an’wasan yake da ita, hakan bai hana shi zama mai Ć™anĆ™an da kai ba. Dr Muhammad Salah shine ya bayyana abinda limaimin masallacin ya faÉ—i game da É—an wasan a shafin sa na Facebook.

A cewar limamin Sadio Mane yana da tsadaddiyar mota ƙirar Bentley amma idan ya tashi zuwa masallaci bada ita yake zuwa ba.

Ga abinda limamin yake cewa akan Sadio Mane:

“Sadio yana zuwa masallaci a kai a kai, a gidan sa yana da mota Ć™irar Bentley,amma yana zuwa wurin mu cikin Ć™aramar mota mara tsada. Ba ya fitowa neman suna, kuma baya da girman kai. Har taimakawa yake wurin wanke banÉ—akin masallacin.

Wannan dai ba shine karo na farko da wani halin kirki na É—an wasan
yake bayyana ba, ko a baya an sha kawo labarai kai abubuwan alkhairi da É—an wasan yake yiwa al’umma musamman a Ć™asar sa ta Senegal.

Ba sa shan giya shi yasa ko da yaushe suke da kuzari, kocin Liverpool ya yabi Mo Salah da Sadio Mane kan rikon su da addini

Post a Comment

0 Comments