Rikicin Kayan Noma: Nasan Wanda akaba kayanku na bashin MAGPAMAN ya cinye maku - Abubakar Sulaiman Bujawa Zonal Coordinator Katsina Zone



Tun Bayan daya ga watan October shekara 2022 wasu mambobi na kungiyar MAGPAMAN ake ta cire masu kudi a asusun ajiyarsu na bankin Eco Bank, wanda Kudin suke nuni da cewa ana cire su ne dan biyan bashi na kayan noman masara da aka basu bashi da ga babban bankin Nigeria ma'ana CBN.

Zonal Coordinator kuma tsohon Coordinator Mani L.G Abubakar Sulaiman Bujawa wanda ya samu wakilcin kungiyar MAGPAMAN yace "Wannan kungiya ce ta tallafin noman masara wanda a shekara biyu da ta gabata shuwagabanin mu na kasa suka muka basu jadawalin mutane wanda daga bisani mutane mutum 6605 sukayi nasarar samun wannan bashi, sai dai shugaban mu na kasa Prof. Edwin Uche ya rike kayan mutum 2004 Wanda ya sakar mana kayan mutum 4601.Naso ache State Coordinator da Secretary na jaha da kuma treasurer su cema shi Prof. Edwin Uche ina kayan mutum 2004, to wannan mutum 2004 duk  kuna ciki kuma Shugaban mu na kasa ya rike ma mutum 2004 kaya."

Bujawa ya cigaba da cewa "ga takarda daga national wadda tabada tabbacin za'a tsaidama kowa cire ciren kudin da ake masa.Wanda suke tataunawa da shuwagabanin jahohi da su basu list din wanda suka samu kaya, da wanda basu samu kaya ba kuma ana masu cire-cire duk zaa tsaida kuma abiya wanda aka Cire masu kaya basu.Bujawa yaba wanda aka cire ma kudi  basu san hawa ba basu san sauka ba shawara da su kai kara kotu dan abi masu hakinsu kuma zai shiga gaba ya tabatarma kotu wlh baabasu kaya ba ba kuma ba abasu kudi ba abimasu hakinsu.


Post a Comment

0 Comments