KIWON LAFIYA: Anfani bakwai(7) da namijin goro yake a jikin dan Adam.



1. Namijin goro ya kunshi sunadaran quinones da kolavironwanda ke warkar da
zazzabin cizon sauro a wani bincike da aka
gudanar a shekarar 2010, kuma aka buga a
mujallar Medicinal Plants Research a
Jamhuriyyar Kasar Congo.

2. Bincike ya nuna cewa, sunadaran antioxidants dake cikin namijin goro suna inganta lafiyar Hunhu.

3. A wani bincike da aka gudanar aka
gudanar a birnin New York na kasar Amurka
ya bayyana cewa, yana kawarda cutar idon
nan ta Glaucoma.

4. Amfani da namijin goro yana hana teba da
rage nauyin jiki, domin kuwa yana sanya shan
ruwa matuka.

5. Sunadarin saponin da antibiotic dake
kunshe a namijin goro sukan taimaka wajen
karfi da tasirin kwayoyin cutar kanjamau.

6. Namijin goro yana kara karfin mazakuta ga
maza ma'aurata.

7. A wani bincike da aka gudanar a jami'ar
Obafemi Awolowo ta Najeriya a shekarar
2008 ya bayyana cewa, namijin goro ya kan
cire kasalar jiki tare da kawar da ciwon
gabbai.

Wani amfani da shukar namijin goro ke yi
shine, tana korar micizai daga wuri. Idan ba a
manta ba kuma, Farfesa Maurice Iwu na
Najeriya ya bayyana cewa, za a iya magance
cutar Ebola ta hanyar amfani da namijin goro.

Majiya: inuwar labarai

Post a Comment

0 Comments