Gwamnatin Najeriya ta fara shirin soke rajistar tsohuwar kungiyar malaman jami’o’i ASUU.

Gwamnatin Najeriya ta fara shirin soke rajistar tsohuwar kungiyar malaman jami’o’i ASUU.

Wata majiya a ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta shaidawa wakilin Daily Trust cewa, matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na yiwa sabbin kungiyoyi biyu ragista na daga cikin matakan soke kungiyar ASUU, da nufin duba yajin aikin da take yi wanda ya kawo koma baya ga jami’o’in gwamnati a cikin sama da watanni 7 da suka gabata.

Idan baku manta ba tun a watan Satumba ne gwamnati ta yi barazanar janye rajistar ASUU a matsayin kungiyar kwadago bisa zargin kin gabatar da rahotannin yadda suka gudanar da tsare tsaren ayyukan kashe kudaden su kamar yadda doka ta tanada a cikin shekaru biyar da ta gabata.

Me za ku ce akan wannan yinkurin na gwamnatin Najeriya? Shin ko kuna goyon bayan soke kungiyar ASUU? 

✍️ Comr Abba Sani Pantami

Post a Comment

0 Comments