Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 10 ga Oktoba, 2022 a matsayin ranar hutu domin karamar Sallah na Mulidin wannan shekara na tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da na kasashen waje murnar halartan taron na bana.
Ya shawarci daukacin ‘yan Nijeriya da su kasance cikin nuna soyayya, hakuri, da juriya wadanda su ne kyawawan dabi’u na Annabi Muhammad S.A.W da ya yi misali da su, ya kara da cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya, tsaro a kasar.
0 Comments