Dan takaran Gwamna A Jam'iyyar SDP A Katsina Ya Raba Gudummuwa A Zageyen Maulidin Gari Duka.


Daga Mohammad A. Isa, Katsina.

Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar SDP mai alamar Doki, Alhaji Ibrahim Zakari Talba ya raba kayan arziki a yayin zagayen Maulidin zagayen gari duka da aka gabatar a ranar Lahadin nan.

Kamar yadda wakilinmu ya labarto mana a lokacin da yake zantawa da masu jagorantar rabon kayayyakin, wani Jamilu da Aliyu Basa, sun bayyana masa cewa;  rabon kayan da dan takarar ya yi wa al'umma wanda Muhammad Tukur Makama Bakori ya dauki nauyin aiwatarwa a mamadinsa, an yi ne saboda nuna so da kauna ga fiyayyen Allah Annabi Muhammadu(S)
Har wayau, masu rabon sun kuma bayyana cewa, sun rarraba kayayyakin ne a yankuna Uku na Birnin a wannan rana ta zagayen Maulidin Gari Duka, don dai farantawa al'ummar Annabi kamar yadda dan takarar gwamnan Alhaji Ibrahim Zakari Talba yake da burin yi a ko da yaushe.

Bugu da kari, Aliyu Basa ya kuma bayyana cewa, an buga Katon din ruwa da Lemu kimanin dubu goma (10,000) inda tuni kuma suka jagoranci raba su ga daukacin al'umma masoya Manzon Allah(S) wadanda suka fito kallo da kuma masu zagayen Maulidi a wannan rana.

Su ma jama'a wadanda suka amfana da rabon kayayyakin sanyaya Makogwaron, sun bayyana jin dadinsu matuka bisa ga yadda wannan dan takarar gwamna ya kawo masu wannan gudummuwa a lokacin da makogwaransu ya ke bukatar hakan, inda ya jika masu shi da wadannan kayyakin alheri musamman ma duba da yadda kayayyakin suka zo masu a daidai lokacin da suka fi bukatarsu, wato sa'ilin da makogwaro ke bukatar a sanyaya shi.
Ranar "Zagayen Maulidin Gari Duka" (kamar yadda al'umma ke kiransa), rana ce muhimmiya ga al'ummar garin Katsina masu yin Maulidi, inda jama'a ke fitowa kwansu da kwalkwatarsu wajen kallon zagayen Maulidin Annabi(S), ranar da take a matsayin ranar karshe ta zagayen Maulidi a watan Rabi'ul-Awwal, zagaye "Bugun Tashi" wanda daga shi ba wani sai kuma na wata shekara in Allah ya kai mu.

Post a Comment

0 Comments