Dalilin Da Ya Sa Aka Hana Hamza Sulaiman Takardar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina- In Ji Dr. Musatapha Inuwa

Tsohon sakataren Gwamnatin jihar Katsina kuma wanda ya nemi takarar gwamnan jihar Katsina a jam'iyyar APC a za6en fitar da gwanin da ya gabata, Dr. Mustapha Muhammad Inuwa, ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da ya sa aka hana Kwamishinan muhallin jihar Katsina Honorabul Hamza Sulaiman Wamban Faskari takarar mataimakin gwamnan, saboda kawai a kuntata masa, kuma sai aka dauko wanda sukai takara tare don ya 6ata masa rai aka ba shi wannan matsayin na takarar mataimakin gwamnan.

Dr. Mustapha Inuwa ya yi wadannan bayanai ne a cikin wani faifan bidiyo da Katsina Media Post News ta kalla.

Ya kuma ambaci cewa jam'iyyun adawa PDP da NNPP duka sun masa tayin shiga cikin jam'iyyunsu, kuma sun masa alkawuran manyan jam'iyyu amma ya mayar masu da amsar cewa shi dan APC ne.

"Don a 6ata mana rai aka ki ba wanda muke ganin in an ba shi maslaha ce. mu muna son shi, gwamna yana son shi, kuma ko ba ka kaunar Allah ka san Hamza a siyasar Katsina ba abin yadawa ba ne." In ji shi.

Ya ci gaba da cewa "Ba Funtuwa kadai ba, Katsina da ko throughout zone din nan ka san (Hamza Sulaiman yana da mutane, kuma yana ganin mutuncin mutane kuma yana da rufin asirin da zai taimaki siyasar." Ya bayyana.

Ya kara da cewa "To amma don saboda da dai a kuntata wa su Mustapha Inuwa aka ki ba Hamza sai aka dauko Faruku wanda shi ya fito takara don ya bata mana rai."

"In ban da rashin ƙwaƙwalwa ta tunani irin ta siyasa, ya za ai Local Government ta tsaida dan takarar gwamna, kai ka tsaida mata mataimaki? Su mutanen dabbobi ne? In ka bi wannan za ka sami gwamna, in ka bi wannan za ku sami Deputy. Takaninku da Allah duk wanda ke nan wanne za ku bi? Mutumin nan kau ko ɗan gidanku ne, saboda ka san abin da gwamna ke yi ka san abin da mataimakin gwamna ke yi." Ya nusar.

Post a Comment

0 Comments