Da Dumin ta: Gwamati Taware Naira Biliyan 470 Cikin Kasafin Kudi Domin Biyan Daya Daga Cikin Bukatun ASUU


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an ware naira biliyan 470 domin farfado da jami’o’i a kasafin kudin shekarar 2023.

Bayar da kudade don farfado da jami’o’in gwamnati na daga cikin bukatun kungiyar malaman jami’o’in (ASUU) da ta shiga yajin aikin tun watan Fabrairu.

Yayin da yake gabatar da kididdigar kasafin kudin shekarar 2023 na Naira Tiriliyan 19.76 ga taron hadin gwiwa na Majalisar, a ranar Juma’a, Buhari ya sabunta rokon da ya yi ga malaman jami’o’in da su kara nuna godiya ga halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu da kuma komawa aji.

Shugaban, ya ce dole ne jami'o'i su nemo hanyoyin samun kudade maimakon dogaro da kasafin kudin gwamnati kawai.

Sai dai ASUU da ke neman Naira Tiriliyan 1.2 a baya ta yi watsi da kudirin na Naira biliyan 150 da gwamnatin tarayya ta gabatar na kwata na farko na shekarar 2023.

Post a Comment

0 Comments