APC Ta Sanya Ranar Litinin Ranar Fara Gangamin Yaƙin Zaɓen Shugaban Ƙasa


Jam’iyyar APC mai mulki, za ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 a hukumance a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridar Vanguard ta jiyo.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar da majalisar yakin neman zabenta ke shirin karbar dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ke da da dawo wa kasar.

Vanguard ta bayar da rahoto na musamman a yau Talata cewa ana sa ran Tinubu, wanda ya yi kwanaki a Landan zai dawo Najeriya cikin makon nan.

Post a Comment

0 Comments