Daga Comr Nura Siniya
Shugaba Muhammadu Buhari zai karrama hamshaƙin Ɗan kasuwa shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max-Air da kamfanin gine gine da tsare tsare na Afdin Construction, Alhaji Ɗahiru Mangal da lambar girmamawa ta CON ciki har da wasu manyan ƙusoshin gwamnati a Najeriya.
Gwamnatin za ta karrama Alhaji Ɗahiru Mangal ne, a matsayin ƙwamandan oda na Nijar wanda yake bada gudunmawa ta fuskar gina ƙasa da bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.
A cikin wata wasika daga ministan ayyuka na musamman da huldatayya tsakanin gwamnati Sanata George Akume, ta ce za a gudanar gagarumin bikin karrama su a ranar 11 ga Oktoba, 2022 a Abuja.
Allah Ya ƙara girma da ɗaukaka yasa a gama lafiya.
0 Comments