Uban Kungiyar Danmarke Restoration Vanguard FKD Alh Murtala Jagal ya fadi dalilinsu na kirkiro wannan kungiya bakomai bane fache kawo yadda jam'iyyar PDP zata lashe zaben ta a ko wane mataki na kasar nan.
Alhaji Jagal ya kara da cewa "A kullum hankalina ya Ina za'a taimaki talaka Dan uwana, Shine ma baban dalilin da yasa nadauki Senator Yakubu Lado Danmarke da kuma Surajo Aminu Makera Domin tunanin mu iri daya ne na taimakon talaka Dan uwana, to inaso in tabatar maku da Senator Yakubu Lado yasan da wannan kungiya kuma mun tabatar masa da wannan kungiya xata shiga ta fita har sai taga ya zama gwamnan jihar katsina da izinin Allah, haka shima senator Aminu Makera Muntabatar masa zamu yi iya kokarin da dukiyarmu da karfinmu har sai munga yakai ga Gucci dama sauran yan takarar jam'iyyar PDP gaba daya
Akwai wani Dan Siyasa a nan katsina Bai tara komai ba amma ya tara mutane kuma ya zama ka dangaren bakin tulu dan haka a kullum a taimaki mutane shine gaban mu kuma Senator yakubu Lado yana da burin haka
Alh Jagal yace wannan kungiya tabbas babbar kungiya ce idan kukayi laakari da wasu kungiyoyi sama da ashirin da ta hade da su wanda akwai coordinatocin wadanan kungiyoyi da muka hade dasu kuma zamu basu coordinatoci na kananan hukumomin su.
0 Comments