Ga wasu Abubuwan da ya kamata mutane su sani game da sabuwar Na'urar zaɓe wadda za ayi amfani da ita a zaɓen shekara ta 2023 idan Allah yakaimu
Na farko dai Babu maganar over vorting.
Na biyu:
Babu maganar jiran tsayawa kidayar kuri'u bayan an kammala za6e, saboda kana za6ar Jam'iyyar da kake so, na'urar tana recording ɗinta a cikinta, kuma take zata tura kuri'un wurin tattara sakamakon za6e na jiha da na Ƙasa.
Na uku:
Babu maganar tsayawa tantance masu jifa kuri'a. Da kazo za'a dauki hotonka da computar domin a tabbatar da kaine mai wannan katin za6en, daga nan sai na'urar ta baka damar yin zaben. Saboda haka ba za'a dauki lokaci wurin jifa kuri'a ba, Dan haka za'a kammala za6e cikin lokaci ba sai an kai dare ba.
Na hudu:
Babu maganar amfani da Balot paper wurin jifa kuri'a, saboda akwai alamar kowacce Jam'iyyar wanda mutum yake so a cikin wannan na'ura. ka na za6en Jam'iyyar da kake so, zata fitar da slip ko kuma ince Ballot paper nata na kanta, kuma ta saka shi cikin akwatinta da kanta.
Na biyar:
Babu maganar invalid a wannan za6en na 2023. Saboda duk alamomin jam'iyun Najeriya suna a cikin wannan na'ura, idan ma baka iya amfani da ita ba za'a gwadama yanda zaka za6i jam'iyar da kake so.
Na shida:
Babu maganar yin za6e sau biyu. Ma'ana kayi za6e ka dawo ka kuma yi. Saboda da zaran wannan na'ura tayi maka hoto kuma kayi tumprint, to babu yanda zakayi kayi za6e sau biyu, koda kuwa ka koma wata rumfar zaɓen ne. Saboda kana zuwa daga anyi ma hoto kuma kayi tumprint na'urar zata fidda bayananka cewa kayi za6e a wata rumfa kuma bazata ta6a baka dama kayi wani ba, saidai kayi hakuri.
Abu na bakwai da ya kamata a sani akan wannan Na'ura shi ne, Babu yadda za'ayi wani yayi za6e da kuriar wani. Saboda kana kara katinka a jikin na'ura, za ta daukeka hoto, kuma zata yi searchig dan ta gano idan katin nakane ko ba naka bane. Idan naka ne sai tabaka dama kayi zaɓe, idan ba naka bane, sai 'yan sanda suyi awon gaba dakai.
Allah ya sa a yi zabe lafiya ya kuma bamu shugabanni na gari.
0 Comments