Za A Fara Gasar Wasan “Table Tennis” Tsakanin Kafafen Watsa Labarai A Katsina.

 


Ranar 21 ga watan Satumbar wannan shekarar ne za a fara buga gasar wasan Table Tennis mai suna kofin Kanwan Katsina a sakatariyar kungiyar yan jaridu ta Najeriya da ke cikin birnin Katsina da misalin karfe 11:00AM na rana.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar marubuta gasar wasanni ta Najeriya SWAN reshen jihar Katsina Nasir Sani Gide ya fitar.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Kungiyar yan jaridu ta Najeriya reshen jihar Katsina hadin gwiwa da kungiyar marubuta gasar wanni ta Najeriya (SWAN) reshen jihar Katsina suka shirya gasar wasan tsakanin kafafen watsa labaran jihar Katsina.

Sanarwar ta ce, za a buga gasar ne tsakanin kafafen watsa labarai da suka hada gidan talabijin na jihar Katsina, gidan radiyon jihar Katsina, ma’aikatar watsa labarai da kuma reshen kungiyar yan jaridu ta Najeriya masu aike wa da rohoton reshen jiharKatsina.

Sauran su ne: Gidan talabijin na kasa da ke Katsina NTA, gidan radiyon Alfijir FM da ke Katsina, gidan radiyon Vision FM da ke Katsina, gidan radiyon tarayyar Najeriya da ke Katsina (Companion FM) da kuma gidan radiyon Martaba FM da ke Funtua, inji jaridar Popular News Hausa.

Sanarwar ta ce gasar na cikin shagulgulan makon yan jaridu da ake a Katsina.

Post a Comment

0 Comments