Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gargadi 'yan Siyasa akan gurbatattun rahotanni.

 


Hukumar yaki da cin yanci da rashawa mai zaman kanta a Najeriya ICPC ta gargadi 'yan Siyasa akan rubutun batanci da kazafi ko aika masu da gurbataccin rahotanni don bata takwarorinsu masu neman mukaman Siyasa. ICPC tace wasu 'yan siyasar suna amfani da gurbataccin rahotanni domin cimma gurinsu na Siyasa

Shugaban hukumar ta ICPC Farfesa Bolaji onwasemi yayi wannan gargadi a babbar Hedkwatar dake Abuja lokacin da ya amshi bakuncin kungiyar gamayyar jam'iyyun Siyasa IPAC a karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Yabaji Sani.

Farfesa Bolaji Owasemi yace irin wadannan halaye da 'yan Siya ke nunawa na son tilastawa hukumar da korafe-korafe na karya domin su samu galaba a kan abokan hamayyarsu, Bolaji yace hakan ba zai samu karbuwa ba ga hukumar ta ICPC ganin yanda ake gaf da gudanar da babban zabe a kasar. Shugaban na ICPC yace hukumar sa tanada kyakkyawar alaka tsakaninta da hukuma zabe mai zaman kanta INEC a kan yanda za'a tantance duk wani korafi na gaskiya a lokacin da bukatar hakan ta taso Farfesa ya bukaci jam'iyyun Siyasa da su tabbatar da sun tantance duk wasu masu yimasu takara, kasancewar ko wace kasa suna zabar mutanen da suka cancanta ne.

A jawabin shugaban kungiyar gamayyar jam'iyyun Siyasa ta kasa IPAC yabaji sani yace manufofin ziyarar itace;  Asamu goyon baya daga ita hukumar domin ganin yanda zabe ke tunkarowa.



Post a Comment

0 Comments