Rundunar 'Yansanda ta kama 'Yanfashi da makami da masu garkuwa da Mutane, Katsina

A ranar Laraba 31 ga watan Agusta rundunar 'yansanda a Katsina ta bayyana mutane goma sha tara, da ake zargi da laifuka daban-daban. Da yake gabatar da jawabinsa ga manema labarai, Kwamishinan 'Yansanda na jihar Katsina. CP  Idris Dauda Dabban ya bayyana, gungun 'Yan fashi da makami barayin Motoci da aka kamo daga jihar Kano, Bauchi, Jos da Katsina, da masu garkuwa da mutane guda bakwai daga karamar hukumar Danja. Ansamu Motoci guda goma sha uku, da Rasidin mota da suke hadawa na boge da hatimin da suke bugawa Rasidan. Akwai sauran nau'ikan makamai Irinsu Adduna wukake da makullen motoci, da Filat Number. 

A wani samamen kuma rundunar 'yansanda ta jihar Katsina a ranar 12 ga watan Agusta sun dira maboyar 'yan bindiga a garin Babban Duhu dake karamar hukumar Safana, inda suka isa maboyar masu garkuwa da mutane, suka samu bindiga AK47 da alburusai. Rundunar ta ce tana nan tana tsananta bincike akan lamarin

Da yake karin haske akan masu laifin kakakin Rundunar 'Yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya bayyana wadanda ake zargin daya bayan daya da kuma laifukan da ake zargin sun aikata, kuma wasunsu sun tabbatar da laifin nasu a gaban manema labarai.








Post a Comment

0 Comments