"Mu na Fatan ba zaku kasance masu lalata tarbiya ba"
Sakataren din-din-din na ma'aikatar watsa labarai
Ga Kungiyar Masu Shirya Finafinai MOPPAN reshen jihar katsina
Suleiman A Suleiman Zamani Media Crew✍️
A bisa wata ziyara ta musaman da kungiyar Motion Picture Practitioners Association Of Nigeria MOPPAN reshen jihar katsina ta kaima sakataren Din-din-din na ma'aikatar watsa labarai Alh Sani Bala Kabomo ta kaimashi, kungiyar ta bukaci wannan ma'aikatar ta watsa labarai ta duba yiwuwar ansa masu wasu bukatu da suka zo dasu.
Shugaban kungiyar Lawal Rabe Lemoo yayi ma sakataren din-din-din bayanin alakarsu da wannan ma'aikata tun kafin zuwan shi a matsayin sakataren din-din-din a ma'aikatar ya fadi tsananin Alaka mai kyau dake tsakaninsu da wannan ma'aikatar, Lawal Lemoo yace "babban makasudinmu na kawo wannan ziyara dan tayaka murnan samun wannan makami da kuma wasu yan bukatu da muka zo dasu a gareka Wanda suka hada da:
Neman ofishin din-din-din na wannan kungiyar Wanda wasu jahohi sukan ba takwaranmu ofishi a ma'aikatar al'ada ta jaha idan da hali muma muna so a taimaka mana dashi duba da biyan kudin haya yayi wuya.
Akwai wasu fina-finai da mukayi shekara daya da ta wuce zamu so wannan ma'aikatar ta ba gidan Tv malakar jihar katsina KTTV ta dinga sanyawa dan haskaka taurarin mu na wannan kungiya.
Sakataren Din-din-din na ma'aikatar watsa labarai ta jihar katsina Alh Sani Bala Kabomo yayi godiya a bisa ziyarar da wannan kungiya ta MOPPAN ta kawo mashi, ya kuma ce yana mai fatan bazasu kasance cikin masu lalata tarbiya ba saboda yanzu babu abinda ke tasiri a zukatan mata da kananan yara kamar film, ya kuma tabbatar masu da zai cigaba da kula da ita wannan kungiya kamar yadda sauran sakatarori sukayi Wanda suka gabata.
Dangane da rokon da sukai yana mai tabbatar masu da zai zauna da Darektan fina-finai na wannan ma'aikatar dan duba hanyoyin da za'a biya masu dukan bukatun su da su.
0 Comments