Har yanzu Barcelona ba ta yi wa sabbin 'yan wasan da ta dauka a bana rijista ba, duk da cewar za a fara kakar La Liga ta bana a karshen mako.
A ranar Asabar mai zuwa dai ne Barcelona za ta fara wasan La Liga kakar 2022/23 da kar6ar bakuncin Rayo Vallecano.
Barca dai na fama da matsin tattalin arziki, wanda ya kamata ta magance, domin bin dokar kashe kudi wadda La Liga ta gindaya. Hakan ya sa Barcelona ta sayar da wasu abubuwan da ke kawo mata kudi, don ta samu damar yin rijiristar 'yan wasan da ta saya a bana.
Cikin 'yan kwallon da kungiyar ta dauka a kakar nan sun hada; da Robert Lewandowski daga Bayern Munich da Raphinha daga Leeds United.
Sauran sun hada da Jules Kounde da Andreas Christensen da kuma Franck Kessie.
Har yanzu Barcelona dai na kokarin bin dokar La Liga, inda take yunkarin cefanar da karin wasu abubuwanta, domin samun damar yin rijistar a kan lokaci. Haka kuma tsohon dan wasanta mai tsaron baya, Gerard Pigue ya rage albashinsa.
Mahukuntan La Liga sun yadda cewar wadannan sauye-sauyen da Barcelona ke yi zai ba ta damar yin rigistar sabbin 'yan kwallon, amma ana ganin daya bayan daya za ta yi ba gabaki dayansu ba a lokaci daya ba. Matsin tattalin arzikin da Barcelona ta fada shi ne ya sa har yanzu ba a san makomar Frenkie de Jong.
Manchester United na fatan daukar De Jong, Chelsea ta nuna sha'awar sayen dan wasan tawagar Netherlands.
To sai dai De Jong na bin Barcelona kudi tun daga lokacin da ya rattaba kwantiragi komawa kungiyar, a wannan lokacin ya kamata a biya shi bashin da yake bi kamar yadda aka yi alkawari. Sai dai shugaban Barcelona, Joan Laporta ya jaddada cewar, kungiyar na bukatar tsohon dan kwallon Ajax ya ci gaba da taka leda a Camp Nou.
Barcelona na kokarin sayar da wasu 'yan wasan da suka hada da Samuel Umtiti da Martin Braithwaite, wanda aka yi wa ihu a ranar Lahadi kafin wasan da ta buga da Pumas a Nou Camp.
0 Comments