Muktar Surajo |
Muktar Surajo ÆŠansiyasa ne daga jam'iyyar PDP kuma masoyi ga Yakubu Lado Danmarke, da ya shirya gasar kwallon kafa domin sada zumunci ga 'ya'yan jam'iyyar PDP a karkashin kungiyar Ladon Alkhairi ta Dakta Musa Gafai. Inda yace lallai wannan gasa sun mata kyakkyawan shiri da zata zama daya tilo a cikin ko wace irin gasa da akayi ko za'ai a cikin garin Katsina duba da yanayin tsarinta.
Yace saboda an tsarata a ko wane Zone guda uku dake Jihar Katsina, kuma ko ina za a bugata wato Katsina Zone Daura Zone Funtua Zone. Yace a yanzu zasu fara da Katsina Zone.
Muktar ya yi wani albshir ga dukkanin kungiyoyin cewa zasuga Canje-canje da dama akan yanda a a tafiyar da wasanni, tun daga Alkalan wasu. Yace; sannan kuma kamar yanda gasar ta fito tundaga Katsina Zone akwai kungiyoyi talatin da hudu 34 da zasu fafata a cikinta, a kowace ƙaramar Hukuma a cikin garin katsina kuma suka dauki ƙungiyoyi 22. Yace akwai kyautittika masu tsoka, wanda ba a taba yin irinsu ba. Inji muktar surajo. A karshe yayi fatan samun Nasara ga jam'iyyar PDP a ko wane mataki a zabe mai zuwa na 2023.
0 Comments