"Dukda matsin Tattalin Arziki da ake fama dashi Muna yin ayukan Raya kasa a Karamar hukumar kaita"

 "

Dukda matsin Tattalin Arziki da ake fama dashi Muna yin ayukan Raya kasa a Karamar hukumar kaita"

- Engr. Bello Lawal Yandaki Executive Chairman Kaita LG.

Suleiman A Suleiman Zamani Media Crew✍️

A cikin Shiri na musamman da kamfanin Zamani Media Crew ya ke shiryawa a yau 3rd Augus, 2022 Shirin ya samu bakuncin Shugaban Ciyamomi na kananan hukumomi 34 (ALGON) Engr Bello Lawal Yandaki Wanda yayima kamfanin Zamani Media Crew  Bayanin Cigaba da ya Samar ma Karamar hukumar kaita a matsayin shi na Shugabanta.

"A kantoma na Karamar hukumar kaita da na rike na Yi Bakin kokarina wajen Kawo Cigaba a wannan Karamar hukuma tawa kamar gyaran Local Government, gyaran asibitoci, makarantu da sauransu, yanzu Kuma da Allah ya Kawo ni a matsayin Zababen Ciyaman Ina kokarin Cigaba da Kawo ma Karamar hukumata Cigaba ta ko Ina ko yanzu Mun fara kamar gyaran Bohol, gyaran asibitoci da sauransu".

Dukda matsin Tattalin Arziki da ake fama dashi Muna yin ayyukan Raya kasa a Karamar hukumar kaita ta hanyar haraji da Muke samu daga sama duk dai da Sune Muke yin wannan ayyykan.

Shugaban yakara da cewa dangane da harkar Tsaro mu anan kaita Muna kokari wajen Cigaba da Kawo kyakyawan alaka tsakanin makiyaya da manoma duba da yadda Muke zama da shuwagabanin kasa masu rawani Muna tattaunawa Kuma Ana Samun fahimta sosai dukda dai akwai Yar matsala wadda aka samu da Fulani amma Alhamdulilah Karamar hukuma tayi kokari wajen ganin anshawo kan matsalar dawuri.

Engr Bello Lawal yabada haske a kan minene ALGON Wanda yace" ALGON kungiyace ta shuwagabanin kananan hukumomi na Jaha. shi aikin ALGON kamar gidauniyace wadda take tataunawa kan Cigaban kananan hukumomi.

Post a Comment

0 Comments