Alhaji Murta Jagal |
A cikin shirin gangar Siyasa na Zamani Media Crew da take fira da 'Yan Siyasa ma bambanta jam'iyyu daban-daban domin bayyana ra'ayinsu akan al'amuran Siyasa dake faruwa a jihar Katsina, yau shirin na Gangar Siyasa yayi fira da matashin dan Siyasa daga jam'iyyar PDP Alh. Murtala Jagal, inda ya tabo bangarori daban-daban da suka shafi al'amuran Siyasa a jihar Katsina. Murtala ya fara maida raddi ga masu sukar jam'iyyar PDP da cewa sune suka haddasa rashin tsaro a jihar, inda suke cewa APC ta gaji matsalar tsaro. Yace matsalar tsaro ga duk mai hankali ya kama bakinsa yayi shiru gami da addu'a saboda kowa yasan yanda akai mulkin PDP a jihar Katsina da irin abinda ya faru, yace mutanen jihar Katsina sune alkalai.
Da yake tsokaci akan sukar Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a PDP Sanata Yakubu Lado Danmarke, a kan masu cewa Sanatan yana saida takararsa yace, wannan wani zance ne kawai na yarfe saboda Siyasa kowa zai yi yarfe yanda yaga dama. Jagal ya kara da cewa, ai Sanata Lado yayi shugabanci kuma ya kalubalanci masu suka akan aje mahaifarsa agani irin Ayyukan raya kasa, sana kuma game da rike albashin karamar hukuma, ai Sanatan ya bayyana yanda yayi shugabanci kowa yaji.
Murtala Jagal ya yabi kokarin Hon. Musa Gafai akan yanda tunda yabar jam'iyyar APC ya koma PDP Yake ta samun magoya baya a ƙarƙashin Ƙungiyarsa ta Ladon Alkhairi yanda yake ta Kwashe mutane mabiya domin shiga jam'iyyar PDP da aikace-aikace babu kama hannun yaro. Jagal yace lallai musa Gafai irinsu ake so a cikin Siyasa.
A karshe Alhaji Murtala ya yayi godiya ga Dantakarar sanata na jam'iyyar PDP Alhaji surajo Aminu Maƙera bisa kulawa da yanda ya daukeso da muhimmanci har ya tako kafa yazo wajen sana'arsu a madadin jam'iyya PDP da dukkanin 'yan takarar su a matakai daban-daban har izu shugaban ƙasa domin sanin mahimmanci su. Yace yana goyon bayansu. Jagal yayi godiya da wannan.
Akwai cikakkiyar Firar a tashar @Zamani Media Crew TV a tashar mu ta YouTube.
0 Comments