SHARI, 'AR BALA ABU DA MAMUDA MAI ZAMANI
....ZA A SAKE SHIGAR DA KARAR
Daga dama Bala Abu Musawa zuwa hagu Mamuda Lawal |
Mu'azu Hassan @katsina city news
Lauyoyin Bala Abu Musawa Mataimakin shugaban jam 'iyyar APC ta Katsina, sun tabbatar ma, da jaridun katsina city news cewar zasu shigar da sabuwar kara a wata kotun cikin sati Mai zuwa.
Lauyoyin sun ce Wanda ke da karar Alhaji Bala Abu Musawa ya basu umurnin su sake wata kotun kuma su shigar da sabuwar karar neman hakkin É“ata masa suna da akayi, a takardar da Alhaji Mamuda Lawal ya rubuta, akan koken zaben fitar da Dan takarar Dan majalisar wakilai a kananan hukumomin Matazu da Musawa da jam iyyar APC tayi a watan Mayu da ya gabata.
Takardun an baiwa Gwamnan katsina, jam iyyar APC da hukumar INEC da sauran jami 'an tsaro.
A takardar anyi zargin Alhaji Bala Abu musawa ne, ya kawo yan dabar da suka tada hargitsi a wajen zaben, wanda yayi sanadiyar mutuwar wani matashi da jikkatar mutane.
Bala Abu ya Nemi lauyoyin sa da su shigar da karar neman masa hakkin sa a kotu.
A zaman kotun da akayi ranar alhamis din da ta gabata, Alkalin kotun majistire ta uku Alhaji Abubakar Umar ya tsame kanshi daga Shari ar bisa dalilai na kashin kanshi.
Amma yace masu karar suna iya neman wata kotun, su sake shigar da sabuwar kara.
Akan haka, Bala abu musawa ya umurci lauyoyin shi su Nemi wata kotun su shigar da sabuwar karar. Kuma lauyoyin sun ce zasu yi haka cikin satin da za a shiga.
Wata majiya tace mana ana ta kokarin yadda za a sulhun ta maganar ta bayan fage, ba sai an kai Shari a ba.
Bala Abu ya amince da maganar sulhun, amma bisa sharadi. Sharadin kuwa shine Alhaji Mamuda Lawal ya rubuta takardar janye wancan zarge zarge da yayi da amsar kuskuren shi da bashi hakuri a takardar da zai rubuta. Bala ya amince da sulhu a bisa wannan sharadin ko kuma Shari a tayi aikin ta.
Munyi kokarin jin ta bakin Alhaji Mamuda Lawal akan matsayar su na wannan sharadin, Ba muyi nasara ba.
0 Comments